Tuesday 8 March 2011

Masu kunnen }ashi!

A makon jiya, gidan talabijin na CNN ya tambayi ]aya daga cikin ’ya’yan Shugaba Muammar Gaddafi na }asar Libya, wato Saiful-Islam Gaddafi, abin da mahaifin sa da ’yan gidan su za su yi tunda ga shi ’yan }asar su na zanga-zangar }in amincewa da mulkin su. Shin za su tsere ne kamar yadda shugaban Tunisiya ya yi, ko }a}a? Sai ya amsa da cewa: “Mu na da Dabara ta 1, da Dabara ta 2 da kuma Dabara ta 3. Dabara ta 1 ita ce za mu ci gaba da zama har mu mutu a Libya. Dabara ta 2 ita ce za mu ci gaba da zama har mu mutu a Libya. Dabara ta 3 ita ce za mu ci gaba da zama har mu mutu a Libya.”

Manufar sa dai ita ce ba za su ta~a barin Libya ba, sai dai a mutu!

Akwai mutum hu]u a cikin ’yan kwanakin nan da su ka yi kunnen uwar shegu da bu}atar da ’yan }asashen su su ke da ita ta cewa lallai su sauka daga karagar mulki don a fito da tsarin mulki irin na dimokira]iyya a }asashen nasu. Wa]annan mutane su ne Shugaba Zine El Abidine Ben Ali na }asar Tunisiya, da Hosni Mubarak na Masar, da Laurent Gbagbo na Cote d’Ivoire, da kuma na baya-bayan nan, wato Kanar Gaddafi na Jamhuriyar Larabawa ta Libya. |ata lokaci ne in tsaya ina fa]a maku cewa tun tuni biyun farko cikin su su ka ari takalmin kare, su ka arce, sannan sauran biyu sun kafe, sun ce ba za su yarda su bar mulki ba ko da kuwa za a yi asarar rayuka ne. Gbagbo ya na tirka-tirka da abokin hamayyar sa na siyasa, wato Malam Alassane Ouattara, wanda shi ne ya lashe babban za~en da aka yi a }asar amma an hana shi kar~ar ragamar mulki, sannan duk }asashen duniya sun yi Allah-wadai da }e}asa }asar da shi Gbagbo ]in ya yi. Har yau ]in nan ana fafatawa a wannan }asar da ke yankin Afrika ta Yamma. A ranar Alhamis ta makon jiya, an yi musanyar harsasai tsakanin ~angarorin biyu a babban birnin }asar, wato Yamoussoukro. Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar [inkin Duniya (UNHCR) ta ruwaito cewa a}alla mutum 20,000 ne su ka tsere daga sassan birnin Abidjan washegari, su ka nemi mafaka a wasu unguwannin.

Babu ruwan wa]annan mutane masu kunnen }ashi da sauraren wani bahasi ko lalama. Da Ben Ali da Mubarak sun sha alwashin cewa ba za su ta~a sauka daga mulki ba har illa masha Allahu, wai gwamma su yi shahada, to yanzu kuma ga Gaddafi ya na fa]in haka shi ma. Babu shakka, na san akwai ire-iren wa]annan shugabannin da dama a nan Afrika da kuma yankin Gabas ta Tsakiya. To amma mutanen su ba za su sake yarda su na yaudarar su da }aryar cewa su ’yan kishin }asa ne ko kuma masu }in jinin Amurka ba ne. Jama’a sun riga sun }yaro su, ba su bu}atar komai sai sauyi daga mulkin danniya zuwa mulkin dimokira]iyya. Tuni jama’ar }asashen Yemen, Bahrain, da Jodan su ka shiga sahun takwarorin su na Tunisiya; dubban mutane sun fito kan tituna su na zanga-zangar bu}atar sauyin siyasa. Mugun martanin da shugabannin su su ke aika masu, sam, bai karya masu lago ba.

A yanzu dai rikicin }asar Libya wanda duk duniya ta fi sa wa ido saboda muhimmancin sa, ya fara hawa hanyar da rikice-rikicen Tunisiya da Masar su ka hau tun daga watan Janairu. Don haka za mu iya cewa ramin }aryar Gaddafi }urarre ne. Duk da irin cika-bakin da ya ke yi, shi da ]an sa Saiful-Islam, akwai alamun cewa mulki ya soma su~uce masa, tunda ga shi ’yan tawaye sun amshe rabin }asar daga hannun sa. Gwamnatin sa, kamar ta Mubarak, ta ginu ne bisa ru~a~~en kadarkon da iyalan sa da ’yan }abilar sa su ka tallabe. To amma tsawon shekaru 40 da aka yi ana mulkin kama-karya ya sa wannan kadarkon bai da sauran }arko a zamanin yau. Tuni duniya ta sauya, amma su wa]annan masu mulkin danniyar da ke Afrika da yankin Gabas ta Tsakiya sun kasa fahimtar hakan. Ba fa zai yiwu ka ci gaba da mulkar jama’a a tsawon lokaci ba tare da ka take ha}}in ]an’adam ba. Mutane ba za su ci gaba da bu}atar ka ba ko da kuwa ka cimma nasarorin gina }asa kamar yadda Gaddafi ya yi. Za su so su samu sauyi, su ]an sarara.

Shure-shure bai hana mutuwa, Gaddafi zai fa]o }asa warwas domin kuwa dukkan dalilan da su ka sa aka cimma nasara a juyin-juya-hali a Tunisiya da Masar akwai su a wannan kacaniyar ta Libya. Na farko, jama’ar Libya su na zanga-zangar bu}atar ya sauka daga mulki a birane da dama. Na biyu, mutane ’yan asalin wasu }asashen su na ta guduwa daga }asar a yayin da wutar rikicin ke }ara ruruwa. Na uku, wasu manyan }usoshin gwamnatin sa su na ta yin murabus. Sun ha]a da ’yan Tawagar Libya a Majalisar [inkin Duniya a birnin Jeniba, wa]anda su ka aje aiki a daidai lokacin da ake taron Cibiyar Kare ’Yancin [an’adam ta Majalisar [inkin Duniya a ran Juma’a ta makon jiya. Sa’annan su ma ’yan tawagar Libya a taron {ungiyar {asashen Larabawa (Arab League) sun aje aiki a birnin Al}ahira ran Juma’ar makon jiya, su ka ce su yanzu wakilan talakawan Libya ne ba na Gaddafi ba. Na hu]u, manyan }asashen duniya, wa]anda duk mai mulkin danniya zai bu}aci tagomashin su, sun juya wa Gaddafi baya. Akwai ha]in gwiwa a tsakanin su kan yadda za a tunku]o da gwamnatin sa, ta hanyar yin amfani da hanyoyin diflomasiyya da na kafafen ya]a labarai. Shi ya sa a kowane lokaci ba labarin da ake yi a manyan tashoshin talabijin na duniya irin su CNN da Aljazeera da BBC World sai na Libya. Hakan ya taimaka wajen harbo gwamnatocin danniya na Tunisiya da Masar. {asar Faransa ta bayyana }a}aba wa Libya takunkumin karya tattalin arziki. Amerika da Birtaniya sun janye goyon bayan su ga Gaddafi.

Majalisar [inkin Duniya, ta hanyar cibiyoyin ta, ta kafa wa Libya }ahon zu}a. Misali, Hukumar Ciyar da {asashe Gaba ta Majalisar [inkin Duniya (UN Development Programme) ta kori ]iyar Gaddafi, wato Aisha al-Gaddafi, daga mu}amin jakadar musamman, ba don komai ba sai saboda ya}ar ’yan zanga-zanga da ake yi a Libya. Shi kan sa sakatare-janar na majalisar, wato Mista Ban Ki-moon, ya fito }arara ya ragargaji Gaddafi saboda yin watsi da ya yi da kiran da ya yi masa na ya daina harbe masu zanga-zanga. Cibiyar Kare Ha}}in [an’adam ta Majalisar [inkin Duniya ta yi taro a birnin Janiba na }asar Siwizalan inda aka fitar da kakkausar suka kan Libya.

Duk a wannan har}allar, munafinci da rashin tsare amana na }asashen Turai da Amurka sun fito fili. Misali, mun san cewa Amurka da Tarayyar Turai sun sha ]aure wa azzaluman shugabanni gindi, musamman a Afrika da Gabas ta Tsakiya, ba don komai ba sai don su na biya masu bu}atun su. Bu}atun sun ha]a da ba su damar sayen man fetur arha, da ba su ha]in kai kan matsalar ’yan ci-rani da ke shigar masu }asa, da tsaro na yankuna, da ya}i da ta’addanci da kuma hana bun}asar addinin Musulunci a fa]in duniya. To amma da zarar sun ci moriyar ganga sai su yada kwauren ta. Da ma Gaddafi ba nasu ba ne, ba kamar Mubarak ba. Da ma su na kallon sa a matsayin ]an taratsi. To sai ga shi kuma ya shiga uku. Don haka kun ga sun samu damar da za su bi duk hanyar da za su bi don su kakka~o shi daga she}ar sa. Saboda haka dai masassarar da ta ci shugaban Tunisiya da na Masar ba za ta bar shi ba; abin da ya ci Doma, ba ya barin Awai. Ko ya so ko ya }i sai mulki ya koma hannun talakawa, wato mulkin dimokira]iyya.

No comments: