Thursday 23 September 2010

Matasa da tashin-tashina

Ba tun yau ba aka san cewa ]aya daga cikin manyan matsalolin Nijeriya shi ne rashin aikin yi, sannan wannan matsalar ta na ba da gudunmawa ga tashe-tashen hankula na }abilanci da na addini a cikin ’yan shekarun nan. A makon jiya, wani muhimmin rahoto da cibiyar ya]a al’adun }asar Birtaniya, wato British Council, ta ]auki nauyin yin sa ya yi garga]in cewa idan har Nijeriya ba ta samar da guraben aikin yi guda miliyan 25 a cikin shekaru 10 masu zuwa ba, to, tashe-tashen hankula da matasan mu ke yi za su }aru matu}a. Idan har mu ka yi kunnen uwar shegu da wannan rahoton, kaicon mu!

Wasu manyan ’yan Nijeriya wa]anda su ka ha]a da tsofaffin ministoci da kuma masanan harkokin tattalin arzikin }asa, irin su Ngozi Okonjo-Iweala, Frank Nweke Jr., Lami]o Ado Bayero, Donald Duke, Pat Utomi da Maryam Uwais, su ne su ka yi bincike su ka rubuta rahoton mai suna “The Next Generation Nigeria”. Haka kuma wasu masanan daga Amerika da Ingila sun taka rawar gani wajen ha]a rahoton. A ranar Larabar makon jiya aka yi taron }addamar da shi a Abuja. Tsohon Ministan Ya]a Labarai, Mista Frank Nweke, Jnr., shi ne ya karanta gundarin abin da rahoton ya }unsa a gaban jama’a. Ya ce rahoton ya gano cewa Nijeriya ta na fuskantar “barazanar yawan jama’a” saboda rashin aikin yi tsakanin matasa. Rahoton ya }ididdige cewa yawan mutanen Nijeriya zai }aru daga mutum miliyan 150 da ke akwai yanzu, da }arin mutum miliyan 63 ya zuwa shekarar 2050. Hakan zai sa Nijeriya ta kasance ta biyar a cikin }asashen da su ka fi yawan jama’a a duniya. Rahoton ya hango cewa kashi 40 cikin ]ari na ’yan Nijeriya matasa ne, wanda hakan zai sa a samu }arin ]imbin masu bu}atar aikin yi a nan gaba.
Wannan rahoto dai ya nuna cewa yawan mutanen Nijeriya ya ninka a cikin shekaru ashirin da su ka gabata, wanda ya saka }asar cikin mayuwacin hali idan har ba a dage wajen gyaran koma]ar tattalin arziki ba. Ya ce, “Samun ]imbin matasa marasa aikin yi yakan jefa al’umma cikin halin }a}a-ni-ka-yi, ta hanyar yawaitar aikata laifuffuka da kuma samar da yanayin da zai jawo tashin-tashina. Duk }asar da ba ta shirya wa yin amfani da albarkar yawaitar matasan ta ba, za ta samu kan ta cikin fitinar yawan jama’a, maimakon ta ci moriyar hakan.”

Idan mun lura, wannan rahoton bai tsaya kai da fata kan cewa bala’i ka]ai ya hango ba, a’a, ya ba mu shawarwari kan hanyoyin da za mu bi don kauce wa bala’i. Ya yi la’akalari da cewa za a iya amfani da matasa don gina }asa, tare da nuna cewa matasan mu su ne albarka mafi girma da Nijeriya ta ke da ita, ba man fetur ba. Ya ce: “Matasa su ne albarka mafi girma a }asa, ba fetur ba, a cikin }arni na 21. Idan }asar ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen tattalin arziki kamar yadda ta ke yi a yanzu, ta inganta harkar ilimi, ta samar da ayyukan yi, to, kowane ]an Nijeriya zai iya samun ninkin arzikin sa har sau uku kafin shekara ta 2030, sannan sama da mutum miliyan 30 za su fice daga }angin fatara.”

Rahoton ya ba da shawarar cewa tilas ne }asar mu ta fito da tsari mai kyau don samar da aikin yi a shekaru masu zuwa. Ya ce: “Idan Nijeriya ta kasa yin tsari don inganta rayuwar matasa a nan gaba, za ta fuskaci manyan matsaloli da za su ~ullo a dalilin yawaitar matasa masu jin haushin cewa ba su da aikin yi. Saboda haka za su iya zama wani abu da zai kawo barazana ga zaman lumana a }asar.”

A gaskiya, rashin aikin yi a tsakanin matasan }asar nan ya zama abin ban-tsoro a yau. Gwamnati ta ce wai kashi 20 cikin ]ari na matasan ne ba su da aikin yi, amma duk mai hankali ya san cewa zai kai kashi har 60 cikin ]ari, musamman da yake yawancin masana’antu sun ruguje, sannan bankuna su na ta korar ma’aikata. Na kan ji zafi matu}a idan yaran da su ka gama jami’a ko wata babbar kwaleji su ka same ni don in taimaka in sama masu aiki. Babu aikin. A shekarun baya, lokacin duniya ta na kwance lafiya, ma’aikatu neman matasa su k yi don su ba su aiki. Musamman za ka ga kamfanoni su na zuwa jami’o’i da kwalejoji, su na ]aukar sunayen ]aliban da su ka kusa fita daga makaranta domin su ba su aiki da zarar sun }are. Hakan ta faru kafin zuwan tsarin tsuke bakin aljihu (SAP), da cikin hanci da rashawa, da kuma dur}ushewar tattalin arziki na duniya. Duniya juyi-juyi, kwa]o ya fa]a cikin ruwan zafi.

Babban ofishin }ididdiga na }asa (FOS) ya bayyana cewa yawancin marasa aikin yi, a biranen mu su ke. Sannan wani rahoto da Bankin Duniya ya wallafa ya ce yawancin matasa marasa aikin yi da wa]anda su ka gama makarantar sakandare ne. Ga kuma ]imbin jama’a a karkara su na zaman warabbuka, ba abin yi sai kame-kame da kunge-kunge.
A gani na, ba sai an bi tsarin }ayyade iyali ba don kurum a rage yawan ’yan Nijeriya, kamar yadda rahoton British Council ya ce a yi. Dubi }asar Chaina mana, wadda ta fi kowace }asa yawan jama’a. Chaina, mai mutum biliyan 1.3, har ta zarce Japan wajen }arfin tattalin arziki, ta zama ta biyu a duniya (bayan Amerika). Ita ma Indiya, mafi yawan jama’a ta biyu a duniya, haka ne. Me ya sa? Dalili shi ne su na da shugabanni masu son ci-gaban jama’ar su, ba wawura ba ko bin tsarin }asashen Turawa.
Ai jama’a albarka ce. Kada mu ji tsoro don jama'ar mu na }ara yawa. Dalili shi ne mu na da albarkatun }asa masu tarin yawa da za a iya amfani da su wajen ciyar da }asar mu gaba. Duk inda ka waiga a Nijeriya, ba abin da idon ka zai gane maka sai albarkatu iri-iri. Tun daga sararin samaniya mai cike da hasken rana, har zuwa }asar noma mai dausayi wadda ke }unshe da ma’adinai, ga dabbobi, suke-shuke, mai, da sauran su, sannan ga jama’a masu ji da lafiyar jiki, masu ilimi da son aiki tu}uru. To, amma matsalar mu ita ce ba a yin amfani da wa]annan albarkatun ta hanyar da ta dace. Ana banzatar da su ne. Mu na da yawaitar ~arayi masu sace albarkatun don kurum Allah Ya ]ora su a kai, sannan su na amfani da jama’ar - musamman matasa - wajen ayyukan assha, irin su karuwanci da kuma rikicin addini ko }abilanci.

Shugabannin mu sun yi watsi da aikin noma, sun maida hankali ga man fetur, wanda ya sa sun kasa fahimtar alfanun da ke }unshe jingim cikin sauran albarkatun da Allah Ya ba }asar nan. Ba su ba harkar ilimi muhimmanci, wadda ita ce }ashin bayan gina }asa mai nagarta. Muguwar fa]uwar da ’yan makaranta su ka yi a jarabawar WAEC kwanan nan hujja ce da ke nuna cewa shugabannin mu ba su tunanin abin da ya dace da ci-gaban }asa. Hujja ce da ke nuna irin ha]arin da mu ke fuskanta - wato ta al’umma marasa ilimi ko makamar aiki, wadda za ta iya jawo rigingimu a }asa a kowane lokaci.
Rahoton na British Council ya kuma gano wani abu da ya kamata shugabannin Arewa su sani: wato duk da yake an san cewa har yanzu jahilci }aruwa ya ke yi, tazarar da ke tsakanin sashin Kudu da na Arewa na }asar nan ya na }ara }aruwa ne. ’Ya’yan Arewa sun fi samun shiga makaranta fiye da na Arewa.

Barazanar cewa rigima ta na nan tafe sai }aruwa ta ke yi a yayin da za~en 2011 ya ke }aratowa. Rashin aikin yi ya }aru saboda dur}ushewar da masana’antu su ka yi a sanadiyyar rashin wutar lantarki. Hakan ya sa a yau akwai bataliyoyin matasa marasa aikin yi, su na jiran kawai a ]auke su aikin tada husuma. Masu ]aukar su aikin rigimar ba wasu ba ne illa shugabannin mu wa]anda su ka wawuri dukiyar jama’a kuma za su yi amfani da ita don za~en ta hangar }arfi.

Abin ban-haushi, maimakon ka ji ana maganar samun ’yan takarar da za su magance manyan matsalolin }asar nan irin su rashin aikin yi, an koma kawai ana cacar baki kan tsarin kar~a-kar~a na PDP. Manufar wannan tsari fa kawai wanene zai zama shugaban }asa, kuma daga ina ya fito, ba wanene zai yi }o}arin magance ]imbin matsalolin }asar nan ba.

---
An buga a jaridar LEADERSHIP HAUSA

No comments: