Saturday 28 August 2010

Muryoyin Zuciyar Sa’adatu Baba




Daga Ibrahim Sheme

Fitacciyar marubuciyar nan Malama Sa’adatu Baba Ahmad ta wallafa sabon littafi na wak'ok'in Hausa mai suna ‘Muryoyin Zuci.’ Littafin, mai shafi 80, ya na d'auke da rubutattun wak'ok'i har guda 30. An kasa su zuwa gida uku, inda kashi na 1 ya ke d'auke da wak'ok'i shida, shi ma kashi na 2 wak'ok'i shida, sai kashi na 3 mai wak'ok'i 18.

Wad'annan wak'ok'i, kamar yadda za mu kawo maku nazari a kan su nan gaba kad'an, sun ginu ne bisa jigogi daban-daban na rayuwar mu ta yau. Amma sun fi karkata ne ga fad'akarwa kan rayuwar duniya da buk'atar yin tanaji don rayuwar gobe k'iyama. Akwai wasu da aka yi su kan wasu mutane da marubuciyar ta sani ko ta ji labarin su, kamar marigayi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi, da k'awar ta Talatu (Carmen McCain) da wata Halima, da Farfesa Attahiru Jega, da wasu ’yan unguwar su marubuciyar, wato Fagge, wad'anda su ka riga mu gidan gaskiya, da dai sauran su. Shi ma gidan rediyon Freedom na Kano ba a bar shi a baya ba, an wak'e shi.

Masana biyu sun yi gabatarwar littafin. Na farkon su shi ne Dakta Yusuf M. Adamu, sai kuma Farfesa Abdulk'adir D'angambo, dukkan su malamai a Jami’ar Bayero, Kano.
A gabatarwar sa, Dakta Yusuf ya fad'a wa mai karatu abin da kowane kashi na littafin ya k'unsa. Ya yi nuni da cewa kashi na 1 ya k'unshi wak'ok'i ne da su ka shafi Musulunci da gargad'i da kuma ta’aziyya da abokantaka. Wak'ok'in kashi na biyu sun maida hankali ne a kan matsalolin Nijeriya kamar na za~e. Kashi na 3 kuma ya k'unshi wak'ok'i ne da su ka shafi soyayya da mutuwa da rubutu da hassada.

Dukkan masu gabatarwar, wato Yusuf da D'angambo, sun yi la’akari da hikimar marubuciyar da irin basirar ta, musamman wajen amfani da kalmomi da kuma salon wak'ok'i masu k'war d'aya, wanda ba a cika samu ba a fagen rubutun Hausa a yau.

A littafin, har wa yau, wasu masanan guda uku - wato Malam Isma’il Garba, Malam Zulk'ifil Adam Garba Dakata da Malam Bala Muhammad - su ma sun yi sharhi, inda su ka yaba da wannan gagarumin aikin.

Ita dai Sa’adatu Baba Ahmad, wadda mata ce ga Alhaji Shehu Sunusi Bayero, sananniyar marubuciya ce. Ta rubuta littattafan Hausa sama da 20. An haife ta a Kano a ranar 27 ga Yuli, 1984. Ta yi karatun addini da na boko duk a Kano, inda a yanzu haka d'aliba ce a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a Jami’ar Bayero. Memba ce kuma a K'ungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Kano.

--

An buga a LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma'ar makon jiya


Hoton da ke sama: Sa'adatu Baba ce tare da mijin ta Alhaji Shehu Sunusi Bayero

No comments: